China, inda ta kashe dubban mutane kafin ta yadu zuwa sauran sassan duniya, mutane daban-daban ke yin kira ga attajirai da 'yan kasuwa masu zaman kansu da ma manyan kamfanoni, su bayar da gudunmawa domin yaki da cutar.
Ya zuwa ranar Juma'a 27 ga watan Maris na 2020, alkaluma daga Jami'ar Johns Hpkins da ke Amurka, sun nuna cewa fiye da mutum 558,00 suka kamu da cutar yayin da sama da mutum 25,251 suka mutu.
A Najeriya, ya zuwa ranar Juma'a, cibiyar yaki da cutuka ta kasar ta tabbatar cewa mutum 81 ne suka kamu da koronabairus, uku sun warke, yayin da daya ya mutu a kasar.
gudunmawar biliyoyin naira domin yaki da cutar.
Attajirai irin su Aliko Dangote, Femi Otedola, Abdulsamad Rabiu, Herbert Wigwe da kuma, Segun Agbaje ko wannensu ya ba da gudunmawar naira biliyan daya don a dakile koronabairus
Alal misali, mai kamfanin BUA Group, Abdul Samad Rabiu, wanda ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya kara da cewa baya ga kudin, kamfaninsa ya bayar da kayan aiki da suka hada da injina da na'urorin gwaji da sauransu ga jihohi 9 na kasar.
Hakan ne ya sa hukumomin lafiya da gwamnatoci da ma daidaikun mutane ke yin kira a fitar da kudi da kayan aiki domin dakile koronabairus.
A wani bangaren kuma, ana yin kira ga attajiran da sauran masu wadata su tallafa wa marasa karfi da kayan abinci da abubuwan more rayuwa da ma kudade a yayin da gwamnatoci suke umartar 'yan kasar su zauna a gidajensu don hana baza cutar.
Attajirai irin su Bill Gates, mai kamfanin Microsoft; da Jack Ma, mai kamfanin Ali Baba; da Elon Musk, mamallakin kamfanin motocin Tesla na cikin mutanen da suka bayar da tallafin biliyoyin dalar Amurka da kuma kayan aiki domin yaki da annobar.
No comments:
Post a Comment