Friday, March 27, 2020

Coronavirus a Najeriya: Hanyoyi 4 na kare kai daga cutar

                                    
Mun soma wallafa wannan labari ranar 28 ga watan Fabrairu. Ku latsa alamar lasifika da ke sama domin sauraren hira da Dr. Nasiru Sani Gwarzo kan yadda za ku kauce wa kamuwa da coronavirus:
Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana matakan da mutane za su dauka domin kauce wa kamuwa da cutar numfashi ta coronavirus.
Yaya zan kare kaina daga cutar?
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce:
■ Ku wanke hannayenku da sabulun gargajiya ko sabulun ruwa da ake wanke hannu da shi, wato hand gel, wanda zai iya kashe kwayoyin cuta
■ Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da kyallen fyace majina - sannan ku wanke hannayenku bayan kun yi atishawa domin hana kwayoyin cutar yaduwa.
■ Ku guji taba idanunku, ko hanci ko bakinku- idan hannunku ya taba wurin da cutar ta shafa, za ta iya yaduwa zuwa sauran sassan jikinku.
■ Kada ku rika matsawa kusa da mutanen da ke yawan atishawa ko tari da masu fama da zazzabi - za su iya watsa cutar cikin iska ta yadda ku ma za ku iya kamuwa da ita. - akalla ku matsa nesa da su ta yadda tazarar da ke tsakanin ku za ta kai kafa uku.

No comments:

Coronavirus: Yadda attajiran Nigeria suke bayar da tallafi kan yaki da cutar

China, inda ta kashe dubban mutane kafin ta yadu zuwa sauran sassan duniya, mutane daban-daban ke yin kira ga attajirai da 'yan kasuwa...